Wani Alkali🙄 Da Aka Taba Dayewa Fatar Jiki Kamar Yadda Akeyiwa Rago... 🙆



 Wani Alkali🙄 Da Aka Taba Dayewa Fatar Jiki Kamar Yadda Akeyiwa Rago... 🙆


An taba yin wani sarki da ake kira Cambyses II a daular Farisa A karni na 16th, shekaru kusan 500 kafin zuwan Annabi Isa (a.s)


Shi wannan sarki babu sassauchi a harkarsa ko kadan idan mutum yayi ba daidai ba.


Wata rana  wani alkali a masarautar ya karbi chin hanchi a wajen wani, ya yanke hukunchi na zalinchi da son rai.


Sai labari yaje wajen sarki Cambyses II. 


Bayan sarki ya tabbatar da karbar chin hanchi da kuma yin hukunchin son kai, sai sarkin ya bada umarnin a daye fatar jikin alkalin yana raye a matsayin hukunchin laifuffukan da ya aikata shima. 


Kafin a zartar da wannan umarni, sarkin ya tambayi Alkalin da ya  fadi sunan wanda yake so ya gaje shi a kujerar alkalanchin.


Sai alkalin ya bada sunan dansa, Otanes. 


Sarki ya aminche aka nada Otanes a matsayin sabon alkakin daular. 


Sai aka daye fatar jikin tsohon alkalin a raye, wanda azaba tasa kafin a gama ya mutu.


Da aka chiro fatar, sai sarkin yache a shinfidata akan kujerar sabon alkalin. 


Kullum alkalin idan zai yanke hukunchi sai ya tuna chewa akan fatar babanshi yake zaune,  wanda sarki yasa aka daye saboda karbar chin hanchi da kuma yin hukunchin son kai da zalinchi. 


Comments

Popular posts from this blog

Dalilin Da Yasa WhatsApp Suke Banned Na Number

ClassiQ – “Sume”